logo

HAUSA

AL ta amince da maida Syria mamba a cikin kungiyar

2023-05-08 14:10:48 CMG Hausa

Kungiyar kasashen Larabawa (AL) ta zartas da daftarin kudurin maida da iznin kasancewar kasar Syria matsayin mambarta, yayin taron ministocin harkokin wajen kungiyar da aka kira a jiya Lahadi.

Da yake tsokaci game da batun, babban sakataren kungiyar Ahmed Aboul Gheit ya bayyana cewa, sake ba Syria iznin kasancewa mambar kungiyar AL ba ya nufin cewa, dole ne sauran kasashe mambobin kungiyar su maido huldar diplomasiyya da ita, yana mai cewa, batun ya dogara da burikansu. Ya kara da cewa, ana bukatar karin lokaci domin daidaita batun Syria, batun ya shafi moriyar daukacin kasashen Larabawa.

Har ila yau, ya ce watakila kasashen yamma ba za su yi na’am da kudurin kungiyar ba, amma kasashen Larabawa sun tsai da kudurin ne cikin ‘yanci kuma bisa burikansu. Ya ce moriyar bai daya ta kasashen Larabawa ce ta bukace su tsai da kudurin a wannan lokaci, saboda bai dace kasashen su ci gaba da mayar da Syria saniyar ware ba.

Hakazalika, ya ce za a kira taron kolin shugabannin kasashen Larabawa a ranar 19 ga wannan wata a birnin Riyadh, fadar mulkin kasar Saudiyya, inda za a tattauna kan yadda za a daidaita batun Syria cikin lumana.

A cewar Ahmed Aboul Gheit, shugaban kasar Syria Bashar al-Assad zai halarci taron kolin. (Jamila)