logo

HAUSA

Kasashen Sin Da Afghanistan Da Pakistan Sun Sha Alwashin Karfafa Hadin Gwiwar Inganta Tsaro

2023-05-07 15:41:12 CMG Hausa

Kasashen Sin da Afghanistan da Pakistan, sun bayyana aniyar su ta karfafa hadin gwiwa a fannin tabbatar da tsaro, da yaki da ayyukan ta’adanci.

Kusoshin kasashen da suka hada da ministan harkokin wajen kasar Sin Qin Gang, da takwaransa na Pakistan Bilawal Bhutto Zardari, da mukaddashin ministan harkokin wajen gwamnatin rikon kwarya ta Afghanistan Amir Khan Muttaqi, su ne suka bayyana hakan a ranar Asabar, yayin taron da suka gudanar a birnin Islamabad, fadar mulkin Pakistan.

Yayin da yake tsokaci game da wannan aniya ta kasashen uku, dan majalissar gudanarwar kasar Sin, kuma ministan harkokin wajen kasar Qin Gang, ya ce kasar sa a shirye take ta raba damammakin ta na ci gaba da sauran sassan 2, da sauke nauyin dake wuyan ta na shawo kan kalubalen tsaro tare da kasashen 2, kana tana fatan samar da wani kyakkyawan misali na hadin gwiwar makwaftaka tare da kasashen 2, da kyautata cudanyar rukunin su, da mayar da hankali ga muhimman batutuwan dake jan hankalin su, karkashin kawancen kasashe biyu-biyu, da kuma na jimillar kasashen 3.

Qin ya kara da cewa, bangaren kasar Sin zai shiga hadin gwiwar wanzar da tsaro da yaki da ta’addanci tare da Afghanistan da Pakistan, zai kuma martaba manufar su ta bai daya, karkashin cikakken tarin hadin gwiwa da tsaro mai dorewa, kuma Sin din za ta kalubalanci duk wani nau’in ta’addanci, da raba kafa a manufofin yaki da ta’addanci.

A nasu bangaren kuwa, Muttaqi da Bilawal, sun bayyana cewa, hadin gwiwa tsakanin Sin da Afghanistan da Pakistan, na da matukar muhimmanci a fannin wanzar da tsaro da wadata a yankin su. Sun kuma sha alwashin shiga a dama da su wajen ingiza hadin gwiwar su tare da Sin, tare da samar da wani managarcin tsari na fadada hadin kai a fannonin siyasa, da tsaro da raya tattalin arziki, kana da kare moriyar kasashen 3, ta yadda za su cimma moriyar juna, da samarwa al’ummun kasashen 3 makwaftan juna, da ma na sauran kasashen yankin su alherai masu dimbin yawa.   (Saminu Alhassan)