logo

HAUSA

WHO: Cutar COVID-19 ta daina zama "Batun lafiyar jama’a na gaggawa dake damun da kasa da kasa"

2023-05-06 16:09:01 CMG Hausa

Hukumar kiwon lafiya ta duniya (WHO) ta sanar da cewa, cutar COVID-19 ta daina zama "batun lafiyar jama'a na gaggawa dake damun kasa da kasa", kuma ta soke matakin fadakarwa mafi girma da aka ayyana a ranar 30 ga Janairun 2020.

Babban daraktan hukumar Tedros Adhanom Ghebreyesus ne ya sanar da hakan bisa sakamakon taron da kwamitin kula da batutuwan gaggawa na WHO ya gudanar a ranar 4 ga wata, don tantance yanayin da cutar COVID-19 ke ciki a duniya. 

Tedros Ghebreyesus ya bayyana yayin wani taron manema labarai a jiya Jumma’a cewa, yawan wadanda suka kamu da cutar a duk fadin duniya a baya-bayan nan ya samu raguwa sosai, kuma karfin rigakafi a jikin jama'a ya inganta. Haka kuma, adadin mace-mace ya ragu a kai a kai, kuma matsi kan tsarin kiwon lafiyar duniya ya ragu, sannan galibin kasashen duniya sun koma rayuwar da suka saba a baya.

Ya kara da cewa, "Wannan ba ya nufin cewa cutar da ba za ta kawo barazana ga lafiyar duniya ba."

A cikin shekaru uku ko fiye da suka gabata, duniya ta fuskanci kololuwar annoba da kwayoyin cutar suka haifar, kamar Alpha da Delta da Omicron da sauransu. 

Bisa kididdigar da WHO ta fitar, an tabbatar da jimilar mutane sama da miliyan 760 sun kamu da cutar, yayin da sama da miliyan 6.92 suka mutu. (Safiyah Ma)