logo

HAUSA

Qin Gang ya halarci taron ministocin wajen kasashen kungiyar SCO

2023-05-05 20:59:15 CMG Hausa

Dan majalissar gudanarwar kasar Sin, kuma ministan wajen kasar Qin Gang, ya ce a halin da ake ciki, duniya na fuskantar tarin rigingimu da kalubale, kuma a matsayin ta na muhimmin jigo mai tasiri a harkokin kasa da kasa da na shiyyoyi, ya zama wajibi kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai ko SCO, ta ingiza nasarar “Ruhin Shanghai ", ta gina al’umma mai makomar bai daya, musamman a gabar da harkokin kasa da kasa ke kara shiga yanayi mai sarkakiya da rashin tabbas.

A yau Juma’a ne dai Qin Gang ya yi wannan tsokaci, yayin da yake halartar taron ministocin wajen kasashe mambobin kugiyar ta SCO a birnin Goa na kasar India.

Qin Gang ya kuma jaddada cewa, Sin a shirye take, da ta ci gaba da fadada hadin gwiwa da sauran kasashe mambobin kungiyar, da kara aiki tare, kan turbar bunkasa kasa da kara. Kaza lika za ta ci gaba da aiki da sauran sassa, wajen ganin an cimma manufar gina al’ummar duniya mai makomar bai daya ga dukkanin bil adama.

Yayin taron na wannan karo, mahalartansa sun yi duba na tsanaki kan gudummawar SCO, a matsayin ta na muhimmin dandalin shiyya dake ingiza tsaro da ci gaban yankin ta, sun kuma amince da bukatar kara karfafa hadin gwiwar tsaro, da ingiza hadin kai a sassan da suka hada da na sufuri, da makamashi, da hada hadar kudade, da zuba jari, da cinikayya maras shinge, da raya tattalin arziki ta fasahohin sadarwa.

Bugu da kari, dukkanin sassan sun goyi bayan Afghanistan, a burin ta na tabbatar da kwanciyar hankali da sake ginin kasa, yayin da suke mara baya ga SCO da ta karfafa hadin gwiwa da MDD, da kasashe mambobin kungiyar BRICS, wajen kare manufofi da ka’idojin MDD, da kuma martaba cudanyar dukkanin sassa.  (Saminu Alhassan)