logo

HAUSA

Yawan masu yawon bude ido ya samu karuwa sosai a lokacin hutun murnar bikin ‘yan kwadago a kasar Sin

2023-05-05 09:42:36 CMG Hausa

Daga Asabar da ta gabata, aka fara gudanar da bikin  ‘yan kwadago a kasar Sin, inda aka kwashe kwanaki biyar ana hutu. Mu Sinawa mu kan yi amfani da wannan dama wajen yawon bude ido. Bisa kididdigar da ma’aikatar al’adu da yawon shakatawa ta kasar Sin ta yi, an ce, yawan masu yawon bude ido ya samu karuwa sosai a tsawon wannan lokacin hutu.