logo

HAUSA

Sin ta yi kira da a zurfafa aminci tsakanin kasa da kasa

2023-05-04 15:25:47 CMG Hausa

Zaunannen wakilin kasar Sin a MDD Zhang Jun, ya yi kira ga kasa da kasa da su zurfafa aminci da juna da inganta gina al’umma mai makoma ta bai daya ga bil adama.

Zhang Jun ya bayyana haka ne yayin muhawarar da kwamitin sulhu na MDD ya gudanar kan gina aminci da inganta zaman lafiya mai dorewa a duniya, yayin da ake fuskantar babbar matsala game da hakan a duniya. Ya ce hanya mafi sauki ta kawo tsaiko ga aminci a fannin siyasa tsakanin kasashe ita ce, yin magana ba tare da la’akari da amincin dake tsakanin kasa da kasa ba, da kuma rashin girmama yarjejeniyoyi. Haka kuma hanyar lalata tsaro da aminci ita ce, kafa wani rukuni na neman tsaro da zai iya illa ga sauran kasashe. Har ila yau, ya ce hanya mafi sauki ta lalata dangantakar tattalin arziki ita ce, kawo tsaiko ga tsarin samar da kayayyaki da nuna fuska biyu, da neman yin babakere a bangaren fasaha da danne ci gaba da nasarorin sauran kasashe.

Zhang Jun ya bayyana cewa, wadannan halaye da salon tunani sun saba da kokarin da ake na zurfafa aminci da samar da zaman lafiya mai dorewa a duniya. (Fa’iza Mustapha)