logo

HAUSA

Kwararun kasa da kasa: Ci gaban tattalin arzikin kasar Sin ya zaburar da mutane da yawa a duniya

2023-05-03 16:49:42 CMG Hausa

Asusun ba da lamuni na duniya (IMF), ya fitar da sabon rahoton "Hangen Nesa game da Tattalin Arzikin yankin Asiya da Tekun Pacific" a Hong Kong a jiya Talata 2 ga watan nan, wanda ke kunshe da karin hasashe game da bunkasuwar tattalin arzikin Asiya a shekarar 2023.

Rahoton ya nuna cewa, bisa halin da ake ciki na matsi a yanayin hada-hadar kudi a duniya, da hauhawar farashin kayayyaki a kasashe da dama, da kuma rashin ci gaban tattalin arziki sakamakon tabarbarewar harkokin banki a Amurka da Turai, farfadowar tattalin arziki da kasar Sin ta samu ya ba da babbar dama ga tattalin arzikin yankin Asiya da tekun Pasific.

Sassa da dama dai na da ra'ayi daya da asusun na IMF, inda a kwanan baya ma, masana da kwararru daga kasashe da dama suka bayyana cewa, tattalin arzikin kasar Sin yana daidaita kuma cike da juriya, kana ci gaban sa zai kara samun karsashi, da ingiza ga ci gaban tattalin arzikin duniya baki daya.

Shi ma wani kwararre a fannin yada labarai dan kasar Afirka ta Kudu Kirtan Bhana, ya ce ci gaban tattalin arzikin kasar Sin, ya zaburar da jama'a da dama a duniya, ta yadda sassa da yawa ke neman sabbin dabarun kwarewa daga kasar Sin, kuma hakan ne alkiblar ci gaban duniya, wanda ke karkata ga samun ci gaban duniya a fayyace, bisa cudanyar juna, da kuma hade dukkanin bangarori. (Mai fassara: Bilkisu Xin)