logo

HAUSA

Kasar Sin ta yi kira ga sakatariyar MDD da ta ci gaba da karfafa fannin kasafin kudi na kiyaye zaman lafiya

2023-05-02 19:49:05 CMG Hausa

Mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin a MDD Dai Bing, ya yi kira ga sakatariyar MDD da ta ci gaba da karfafa cikakken tsarin gudanar da ayyukan kasafin kudi na wanzar da zaman lafiya, da karfafa tsarin kula da harkokin cikin gida yadda ya kamata, da inganta ayyukan kiyaye zaman lafiya.

Dai Bing ya bayyana hakan ne a jiya Litinin, yayin jawabinsa a wajen bude taro karo na biyu na kwamitin gudanarwa da kasafin kudi na kwamiti na biyar, na babban taron MDD karo na 77, wanda ya gudana a wannan rana.

A cewar sa, kudi shi ne tushe, kuma muhimmin ginshikin gudanar da harkokin MDD. Kuma a matsayin kasafin kudi mafi girma na MDD, kudaden wanzar da zaman lafiya sun kai biliyoyin daloli. Don haka a ko da yaushe, kasar Sin ke kira ga kwamitin na biyar na babban taron MDD, da ya yi nazari sosai kan kasafin kudin kiyaye zaman lafiya, bisa ka'idojin kimiyya da lura, da samar da albarkatun da suka dace don gudanar da ayyukan kiyaye zaman lafiya yadda ya kamata.

Dai Bing ya kara da cewa, kasar Sin tana goyon bayan kwamitin binciken kudi ya gudanar da aikin sa ido sosai, da ba da shawarwari masu ma'ana, da kuma ci gaba da inganta tsarin tafiyar da kasafin kudi. Kaza lika kasar Sin tana kuma goyon bayan MDD, wajen cika hakkinta na biyan diyya ga kasashen da ke ba da gudummawar sojoji da 'yan sanda cikin sauri. (Mai fassara: Bilkisu Xin)