logo

HAUSA

Bankunan Amurka na ci gaba da fuskantar kalubale

2023-05-01 21:32:55 CMG Hausa

Yayin da karin bankunan Amurka ke fuskantar kalubale, bankin “First Republic” na cikin na baya bayan nan da hankula suka koma kan sa, bayan da bankuna mafiya karfi na 2 da na 3 a kasar suka durkushe.

Darajar hannayen jarin bankin “First Republic” sun fadi da kaso 95 bisa dari, tun bayan fara durkushewar bakunan yankunan kasar a ranar 8 ga watan Maris, kuma masu asusun ajiya a bankin sun janye sama da dala biliyan 100 cikin watanni 3 na farkon shekarar nan, kamar dai yadda wani rahoton jarin bankin da aka wallafa a makon jiya ya bayyana.

Sashen ba da kariya ga harkokin hada hadar kudade, da kirkire kirkire na California ko DFPI, ya ce masu tabbatar da dokoki a fannin sun kwace ragamar bankin “First Republic”, inda banki ya zamo na 3 cikin jerin manyan bankunan Amurka da suka karye cikin watanni 2. Kafin bankin “First Republic”, bankunan “Silicon Valley” da “Signature Bank” ne suka fara durkushewa.

Manazarta na cewa, akwai yiwuwar ganin karin kalubale a fannin hada hadar bankunan Amurka, matakin da suke gargadin na iya kara gurgunta ci gaban tattalin arzikin kasar.    (Saminu Alhassan)