logo

HAUSA

Dan majalisar dokokin Zimbabwe: Ba za a amince da leken asirin da Amurka ta yi wa babban sakataren MDD ba

2023-05-01 16:42:39 CMG Hausa

Wasu rahotannin baya-bayan nan sun zargi kasar Amurka da gudanar da leken asiri kan kasashe da dama, da kungiyoyin kasa da kasa, ciki har da kawayenta, lamarin da ya janyo damuwa, da Allah wadai daga kasashen duniya.

Game da hakan, yayin wata zantawa da wakilin babban rukunin gidan rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG, dan majalisar dokokin Zimbabwe, kana tsohon ministan kula da fasahar sadarwa da tsaron Intanet na kasar, Supa Mandiwanzira, ya ce Amurka tana ikirarin kiyaye matsayi, da amfanin Majalisar Dinkin Duniya, amma ta yabutsa hazo da batun "leken asirin" majalisar. Don haka ya kamata Amurkan ta ba da bayani ga al'ummomin duniya, musamman ma Majalisar Dinkin Duniya kan wannan zargi.

Mr. Mandiwanzira ya kara da cewa, “Sau da yawa Amurka tana amfani da hanyoyin da ba su dace ba, don samun bayanai, da kuma amfani da su wajen yin tasiri kan kungiyoyin duniya. Ba za a amince da leken asirin da ta yi wa babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya ba, saboda kasancewar sa jami’in MDD. Gaskiyar ita ce sauran kasashen duniya su yi taka tsantsan da Amurka. Domin Amurka na neman muradun kanta ne kawai, shi ya sa ta kara yawan jarin da take zubawa a ayyukan leken asiri, tare da lalubo bayanan babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya. Har ila yau, hakan na nuna cewa, hadin gwiwar kasashen duniya da hukumomin leken asirin Amurka na tattare da hadari." (Mai fassara: Bilkisu Xin)