logo

HAUSA

Koriya ta Arewa ta soki lamirin taron Amurka da Koriya ta kudu wanda ka iya haifar da zaman dar dar

2023-05-01 17:00:23 CMG Hausa

Gwamnatin kasar Koriya ta Arewa, ta soki lamirin taron baya bayan nan da Amurka ta shirya tare da Koriya ta kudu, da nufin karfafa hadin gwiwar jibge makamai a zirin koriya, matakin da ka iya haifar da zaman dar dar a yankin.

Mahukunta a Seoul, sun ce yayin taron da shugaban Amurka Joe Biden ya yi da takwaransa na koriya ta kudu a makon jiya, Mr. Biden ya yiwa koriya ta kudun alkawarin haska mata shirin kasar sa, na goyon bayan koriya ta kudun, yayin duk wani rikici daka iya barkewa tsakanin ta da koriya ta arewa.

Kaza lika shugabannin biyu sun amince su karfafa tsaron koriya ta kudu, da ci gaba da jibge na’urorin yaki na Amurka a muhimman wurare dake zirin koriya. Daya daga bangarorin cimma wannan manufa har da rangadin da aka tsara jirgin ruwan yakin Amurka, mai dakon makamin nukiliya zai yi a zirin na koriya, ziyarar da za ta zama ta farko da irin wannan jirgin yaki zai kai zirin tun bayan shekarun 1980.

A cewar kafar watsa labarai ta KCNA mallakin koriya ta arewa, shirin Amurka da koriya ta kudu, ya kunshi hadin gwiwar aiwatar da miyagun matakai kan kasar, kamar dai yadda Choe Ju Hyon, wani kwararren mai fashin baki a fannin tsaron kasa da kasa ya yi tsokaci da hakan. (Saminu Alhassan)