logo

HAUSA

Shugaban Iran: Amurka na lalata tsaro da zaman lafiyar shiyyar

2023-04-30 16:25:14 CMG Hausa

Shugaban kasar Iran Ebrahim Raisi, ya tattauna a jiya Asabar da shugaban kasar Iraki Abdul Latif Rashid da ke ziyara a Iran, inda suka kira taron manema labarai na hadin gwiwa.

Yayin taron manema labaran, Ebrahim Raisi ya yi nuni da cewa, kasashen biyu sun kulla kyakkyawar alaka a fannonin siyasa, tattalin arziki, kasuwanci da al'adu, kuma suna ci gaba da raya dangantakar dake tsakaninsu bisa buri na bai daya. Ya ce a halin yanzu, hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya tsakanin Iran da Iraki a shekara guda, ya zarce dalar Amurka biliyan 10, kuma bangarorin biyu sun amince da ci gaba da fadada mu'amalar tattalin arziki da cinikayya.

Ebrahim Raisi ya jaddada cewa, kasashen biyu sun riga sun rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna kan harkokin tsaro, yana mai cewa, tsaron Iraki na da muhimmancin musamman ga Iran, kuma yarjejeniyar fahimtar juna ta fuskar tsaro da ke tsakanin kasashen biyu tana taimakawa wajen tsaron kasashen biyu da ma duk yankin.

Ebrahim Raisi ya ci gaba da cewa, ko da yake Iran ta yi imanin cewa shawarwarin da ake yi tsakanin kasashen yankin na da matukar tasiri wajen warware batutuwan yankin, kasancewar sojojin kasashen waje musamman na Amurka a yankin, zai gurgunta tsaro da zaman lafiya. Ya bayyana cewa, alakar da ke tsakanin Iran da Iraki ta ginu ne bisa moriyar bai daya, amma Amurka muradunta kadai ta sanya gaba, ba ta damu da muradun Iran da Iraki da sauran kasashen yankin ba.

A nasa bangaren, shugaban kasar Iraki Abdul Latif Rashid ya ce ya yi matukar farin ciki da ganin kyautatuwar dangantaka tsakanin Iran da Saudiyya, kuma kasarsa ta yi imanin cewa, wannan mataki na kyautata alaka zai taimaka wajen samar da zaman lafiya da tsaro a yankin. (Mai fassara: Bilkisu Xin)