logo

HAUSA

Rukuni na biyu na Sinawan da aka kwashe daga Sudan ya isa tashar ruwa ta Jeddah

2023-04-29 20:12:33 CMG Hausa

Da safiyar Asabar din nan ne rukuni na biyu na Sinawan da aka kwashe daga kasar Sudan, ta babban jirgin ruwan sojin kasar Sin, ya isa tashar ruwa ta birnin Jeddah na kasar Saudiyya.

A wannan karon, jirgin ruwan ya kwashe Sinawa 272, da kuma karin ‘yan wasu kasashen kamar Pakistan da Brazil, wadanda yawan su ya kai sama da mutum 200.  (Saminu Alhassan)