logo

HAUSA

MDD da abokan huldarta sun yi maraba da tsawaita dakatar da bude wuta a Sudan

2023-04-29 15:57:03 CMG Hausa

Kakakin MDD ya ce majalissar da sauran abokan huldar ta daga sassan daban daban, sun yi maraba da tsawaita wa’adin dakatar da bude wuta da sassan dake dauki ba dadi a Sudan suka amincewa. Sassan sun kuma yi fatan samar da agajin jin kai ga fararen hular Sudan, yayin wa’adin kwanaki 3 da aka kara na tsagaita bude wutar.

Da yake tsokaci game da wannan ci gaba, kakakin babban magatakardar MDD Stephane Dujarric, ya ce sassan 3, wato MDD da kungiyar tarayyar Afirka AU, da kungiyar raya gabashin Afirka ta IGAD, da hadin gwiwar kasashen Amurka, da Birtaniya da Saudiyya da hadaddiyar daular Larabawa, sun fitar da sanarwar hadin gwiwa, wanda ke na’am da matakin tsawaita dakatar da bude wuta.

Jami’in ya ce bangaren sojojin gwamnatin Sudan, da na dakarun ko ta kwana na RSF, sun tabbatar da aniyar su ta tsawaita wa’adin dakatar da dauki ba dadi, kuma sassan dake fatan samar da tallafin jin kai, na da burin ganin an aiwatar da hakan yadda ya kamata.

Mr. Dujarric ya kara da cewa, sassan sun bayyana farin cikin su, game aniyar bangarori 2 na Sudan, na hawa teburin shawara, ta yadda za a kai ga cimma matsayar dakatar da gwabza fada, tare da tabbatar da cewa an kaucewa jefa fararen hula cikin mummunan yanayi.

Game da samar da agajin jin kai kuwa, Dujarric ya ce MDD da sauran abokan huldar ta, za su ci gaba da kai kayan bukatun gaggawa a duk lokacin da aka samu iko, musamman wadanda suka shafi kiwon lafiya da abinci.  (Saminu Alhassan)