logo

HAUSA

Ministan tsaron Sin ya yi kira da a daidaita batun jagorancin yankin kan iyakarta da Indiya

2023-04-28 20:22:17 CMG Hausa

Dan majalissar gudanarwar kasar Sin kuma ministan tsaron kasar Li Shangfu, ya ce kamata ya yi Sin da Indiya su rungumi matakan kyautata yanayin da ake ciki a kan iyakar su, ta yadda za a cimma nasarar jagorancin yankin yadda ya kamata.

Li Shangfu, ya bayyana hakan ne a jiya Alhamis, yayin zantawarsa da takwaransa na Indiya Rajnath Singh, a gefen taron dandalin ministocin tsaron kungiyar hadin kai ta Shanghai ko SCO, wanda ya gudana a birnin New Delhi na Indiya. Manyan jami’an biyu sun kuma yi musayar ra’ayoyi don gane da batutuwan da suka shafi kasashen su, ciki har da fannin aikin soji.

Li ya kara da cewa, a matsayin su na manyan kasashe makwaftan juna, kuma muhimman kasashe masu tasowa, Sin da Indiya suna da tarin abubuwa na moriyar bai daya, sama da sabanin dake tsakanin su. (Saminu Alhassan)