logo

HAUSA

Kasar Sin ta yi kira ga gamayyar kasa da kasa da su sa kaimin daidaita batun Palasdinu cikin adalci da kuma dorewa

2023-04-26 15:14:46 CMG Hausa

A gun taron kwamitin sulhu, game da batun Palasdinu da aka gudanar a jiya Talata, zaunannen wakilin kasar Sin a MDD Mr. Zhang Jun ya gabatar da jawabi, inda ya yi kira ga gamayyar kasa da kasa da su gaggauta warware batun Falasdinu cikin adalci da kuma yanayi mai dorewa.

Zhang Jun ya kara da cewa, a cikin ’yan shekarun baya, a duk lokacin azumin watan Ramadan, yanayin da ake ciki a yankunan Falasdinu da ake mallaka ya kan jawo hankalin duniya.

A sa’i daya kuma, matakan nuna karfin tuwo na karuwa a yammacin kogin Jordan, ga kuma yanayin da ake ciki a gabashin Kudus, da kuma zirin Gaza da su ma ke kara tabarbarewa. Don haka Zhang Jun ya ce kamata ya yi kasashen duniya su kara mai da hankali, tare da daukar matakai, don gaggauta warware batun Falasdinu cikin adalci, da yanayi mai dorewa.

Ya ce da farko, ya wajaba a nuna rashin amincewa da ayyukan nuna karfin tuwo, da rura wutar rikici a yankin, don tabbatar da tsaro na bai daya. Na biyu kuwa, wajibi ne a daina daukar matakai daga bangare daya, don kiyaye dokokin kasa da kasa. Na uku, a tabbatar da zaman al’ummar yankin, tare da sa kaimin bunkasuwar tattalin arzikin yankin Falasdinu. Na hudu, dole ne a tsaya kan shirin kasancewar kasashe biyu, tare da sa kaimin farfado da shawarwarin wanzar da zaman lafiya. (Lubabatu Lei)