logo

HAUSA

Wakilin kasar Sin a MDD ya yi kira ga kasa da kasa da su rungumi tsarin cudanyar bangarori daban daban

2023-04-25 14:03:21 CMG Hausa

Zaunannen wakilin kasar Sin a MDD Mr. Zhang Jun, ya gabatar da jawabi a jiya Litinin, a gun taron muhawarar kwamitin sulhu game da kiyaye tsarin dokokin MDD da manufar cudanyar bangarori daban daban, inda ya yi kira ga kasa da kasa da su rungumi tsarin cudanyar bangarori daban daban.

Zhang Jun ya ce, na farko ya wajaba a tsaya kan kiyaye ikon tsarin dokokin MDD. Na biyu a tsaya kan tsarin duniya da ke da dokokin duniya a matsayin tushensa. Na uku a kiyaye ikon kasa da kasa na halartar harkokin duniya cikin daidaito. Na hudu, ya zama wajibi a kauracewa daukar matakan kakaba takunkumi daga bangare guda.

Ya kara da cewa, manufar gina al’umma mai kyakkyawar makoma ta bai daya da kasar Sin ta gabatar, ta nuna mana hanyar daidaita manyan kalubaloli, da matsaloli da ake fuskanta a duniyarmu ta yau, kuma kasar Sin za ta yi kokarin tabbatar da shawarar raya duniya, da ta kiyaye tsaron duniya, da kuma shawarar wayewar kan duniya, da ingiza aikin zamanintar da kasar daga dukkan fannoni, kuma ta shiga ayyukan MDD daga dukkan fannoni, don samar da gudummawarta wajen inganta hadin kan kasa da kasa, da tinkarar kalubale na bai daya da ’yan Adam ke fuskanta.  (Lubabatu Lei)