logo

HAUSA

Kasashe da dama sun kaddamar da aikin kwashe jama’arsu daga Sudan

2023-04-25 14:11:07 CMG Hausa

Bangarori masu yaki da juna a Sudan, sun ci gaba da bude wa juna wuta a jiya Litinin, inda aka rika jin amon bindigogi, da harbin igwa a wasu sassan birnin Khartoum, fadar mulkin kasar. Sakamakon haka, kasashe da dama sun kaddamar da aikin kwashe jama’arsu daga kasar.

Ma'aikatar harkokin wajen Jordan, ta sanar a ranar 22 ga wata cewa, daga wannan rana, an kwashe jama’ar Jordan su wajen 300 daga Sudan. Sannan, ita ma ma’aikatar harkokin wajen Masar ta fitar da wata sanarwa a daren ranar 23 ga wata, wadda ke cewa an kwashe Misrawa su 436 daga Sudan a ranar. 

Kaza lika ma’aikatar harkokin wajen Falasdinu ta bayyana a jiya Litinin cewa, an kwashe Falasdinawa 270 daga birnin Khartoum. Bugu da kari, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iraki, ta bayyana a ranar 23 ga wata cewa, Iraki tana kara yin mu’ammala da kasashe makusanta, don hanzarta kwashe jama’arta daga Sudan. 

Ban da wadannan kasashe, kasashen Saudiya, da Amurka, da Ingila, da Faransa, da Japan, da Koriya ta Kudu, su ma duk sun kwashe jami’an diplomassiya da jama’arsu ta hanyoyi daban daban a ’yan kwanakin da suka gabata.

Tun a ranar 15 ga watan nan ne dakarun sojin Sudan da rundunar ko ta kwana ta RSF suka fara dauki-ba-dadi da juna. Kuma bisa alkaluman da ma’aikatar kiwon lafiya ta Sudan ta fitar, an ce, rikicin ya riga ya haddasa mutuwar fararen hula a kalla 400, kuma kusan 4000 sun ji raunuka. (Safiyah Ma)