“Harba Bindiga Kafin Fara Magana” Wane Irin Yanayi Ne Amurka Ta Tsumduma A Ciki?
2023-04-25 17:06:51 CMG Hausa
Daga CMG Hausa
Kwanan nan, wani matashi Ba’Amurke dan asalin Afirka dake kasar Amurka, a lokacin da ya je dawo da kanensa gida, ya shiga wani gida bisa kuskure, inda mai gidan ya harbe shi har lahira.
Yanzu haka, irin wannan rashin tsaro na jefa al’ummar kasar Amurka cikin matukar fargaba, kuma hakan ya faru ne sakamakon karuwar laifuffukan da ake ta aikatawa a cikin ‘yan shekarun baya bayan nan.
A cikin ‘yan shekarun nan, sabani da rikici suna kara kamari a kasar ta Amurka, sakamakon yadda ake fama da rarrabuwar kawuna, da karuwar gibin mawadata da matalauta, da kabilanci da dai sauran matsaloli, lamarin da ya sa al’ummar kasar ke kara fama da rashin tsaro, kuma ba yadda za su yi sai dai su yi kokarin mallakar bindigogi, don neman kare kansu. Tabbas hakan ya jefa kasar cikin wata mummunar da’ira ta rashin tsaro, da sayen bindiga barkatai, da kuma karin tabarbarewar yanayin tsaro.
Idan an yi hangen nesa, muddin dai ba a yi wa tsarin kasar kwaskwarima ba, da wuya a kawar da ainihin sabanin da al’ummar kasar ke fuskanta, a yayin da kuma bindigogi za su kara tsananta matsalolin.
Kasancewar kasar Amurka kasa mafi karfi a duniya, wadda kuma ke daukar kanta a matsayin misali a fannin kare hakkin dan Adam, amma kuma al’ummar kasar ke harba bindiga kafin su fara magana. Shin wa zai kare hakkin wadanda aka harbe su har lahira kafin su fara magana?(Lubabatu Lei)