logo

HAUSA

Seymour Hersh: Makamai da yawa da kasashen yammacin duniya suka tura wa Ukraine sun shiga kasuwar bayan fage

2023-04-24 13:38:47 CMG Hausa

Amurka da kawayenta na gaggauta samar wa kasar Ukraine makamai, don mara mata baya wajen yaki da kasar Rasha. Sai dai a cewar kwararren dan jaridan kasar Amurka Seymour Hersh, makamai da yawa da kasashen yammacin duniya suka baiwa Ukraine sun shiga kasuwar bayan fage, inda ake sayar da su ga ’yan fasa-kwaurin makamai daga kasashe kamar Poland da Romania.

Yayin da yake tattaunawa da tashar talibijin ta RT ta kasar Rasha a jiya Lahadi, Hersh ya bayyana cewa, wannan lamari ya haddasa damuwa sosai, kasancewar mai yiwuwa a iya amfani da makamai masu linzami na tsaron samaniya kirar FIM-92, wajen harbo jiragen sama masu daukar fasinja.

Mataimakin shugaban hukumar binciken manyan laifuffuka a ma’aikatar tsaron kasar Amurka James Ives, ya taba amincewa da yiwuwar aukuwar hadarin bazuwar makaman kasuwar bayan fage.

Kafofin watsa labarai na kasar Rasha, sun gano cewa, ana sayar da wadannan makamai ne kan farashi mai rahusa ta kafar yanar gizo ta sirri, wanda ya fi shahara a fagen cinikin haramtattun bindigogi, da abeben fashewa, da harsasai, da yada haramtattun labarai da ake yadawa a kansa. (Kande Gao)