logo

HAUSA

Sin da Philippine sun sha alwashin bunkasa kawance da hadin gwiwa

2023-04-23 21:30:52 CMG Hausa

Gwamnatocin Sin da na Philippine, sun sha alwashin kara zurfafa kawance, da bunkasa hadin gwiwar dake tsakanin su. Bangarorin biyu sun jaddada wannan aniya ne a jiya Asabar, yayin ganawar shugaban Philippine Ferdinand Romualdez Marcos, da babban dan majalissar gudanarwar kasar Sin, kuma ministan wajen kasar Qin Gang a birnin Manila.

Yayin zantawar, Qin Gang ya ce martaba juna, da abota, da cika alkawura, da rike gaskiya, da gudanar da hadin gwiwa mai ma’ana tsakanin kasashen 2, su ne muhimman moriyar da sassan biyu suka sanya gaba.   (Saminu Alhassan)