logo

HAUSA

An shirya bikin yayata shawarar raya kasa da kasa a hedkwatar MDD

2023-04-21 13:54:39 CMG Hausa

A ranar Laraba 19 ga watan nan ne hukumar hadin gwiwa kan raya ci gaban kasa da kasa ta kasar Sin, da zaunanniyar tawagar wakilan kasar Sin dake MDD, da hukumomin MDD da abin ya shafa, suka shirya bikin yayata manufa cikin hadin gwiwa, mai taken “sabon salon ci gaban shawarar raya kasa da kasa, da sabon matakin ajandar tabbatar da ci gaba mai dorewa”. An gudanar da bikin ne a hedkwatar majalisar dake birnin New York na kasar Amurka.

Shugaban hukumar hadin gwiwa kan ci gaban kasa da kasa ta kasar Sin Luo Zhaohui, ya gabatar da muhimmin jawabi yayin bikin, inda ya bayyana cewa, muhimman shawarwarin da kasar Sin ta gabatar, kamar su gina kyakkyawar makomar bil Adam ta bai daya, da gina shawarar “ziri daya da hanya daya”, da raya kasa da kasa, sun gabatar da dabarun kasar Sin a fannin aikin sake farfadowar dukkanin duniya.

Kaza lika makasudin kokarin ingiza zamanintarwa iri ta kasar Sin wanda kasar ke yi, shi ne samun ci gaba mai inganci, da bude kofa ga ketare bisa matsayin koli, kuma duk wadannan sun tattara fasahohi masu daraja, tare kuma da samar da dabaru na hikima da ake iya koya, karkashin muradun tabbatar da dauwamammen ci gaba.

Luo ya jaddada cewa, idan ana fatan aiwatar da shawarar raya kasa da kasa, ya dace a cimma matsaya guda, a hada kai karkashin jagorancin MDD. A sa’i daya kuma, a gudanar da hadin gwiwa tsakanin kasashe masu ci gaba da kasashe masu tasowa.

Ya ce kasar Sin za ta ci gaba da bin tunanin gina kyakkyawar makomar bil Adam ta bai daya, domin kafa huldar abokantaka tsakanin kasa da kasa, ta yadda za a cimma burin raya kasa da kasa baki daya. (Jamila)