logo

HAUSA

Me Ya Sa Karin Kamfanonin Ketare Suka Samu Ra’ayin Bai Daya Kan Zuwa Kasar Sin Don Raya Kansu?

2023-04-21 21:40:57 CMG Hausa

 

Bisa kididdigar da ma’aikatar kasuwanci ta kasar Sin ta fitar a kwanan nan, an ce yawan kudin jarin waje da kasar ta yi amfani da shi a watanni uku na farkon shekarar bana, ya kai kudin Sin Yuan biliyan 408.45, adadin da ya karu da kaso 4.9 cikin dari bisa na makamancin lokaci na bara, lamarin da ya shaida cigaban tattalin arzikin Sin ba tare da tangarda ba.

A cikin wannan adadi, yawan sabbin kamfanonin ketare ya zarce dubu 10, wanda ya karu da kaso 25.5 cikin dari bisa makamancin lokaci na bara. Yadda kamfanoni ke shiga kasar Sin don kara samun bunkasuwa ya riga ya zama wani muhimmin batu da manyan kafofin watsa labarai na kasa da kasa suke tattaunawa a yanzu.

Akwai hasashen cewa, yawan kudin jarin da za a rika zuba wa sauran kasashe zai ci gaba da raguwa a shekarar 2023. Bisa wannan yanayin da ake ciki, kasar Sin ta sha wuya wajen samun wannan sakamako na jawon jarin waje, amma hakan ba abu ne da ya wuce zato ba. Dalili kuwa shi ne, idan muka duba fannonin da kamfanonin suke zubawa jari, za a iya gano cewa, sun fi zuba wa kasar Sin jari ne a fannonin kimiyya da fasahohin zamani, da karin ingancin masana’antu, a kokarin more damammakin cigaban kasar Sin mai inganci.

A matsayin babbar kasuwa ta biyu ta sayen kayayyaki ta duniya, da babbar kasuwa ta farko ta sayar da kayayyaki ta yanar gizo ta duniya, babu shakka kasar Sin ta zama tamkar wani babban kek ga jarin waje. A waje daya kuma, kasar Sin da ke bude kofarta ga waje, na son more wannan kek na ta tare da sauran kasashen waje, tare da kara girmansa.

Kamfanin Tesla, da Airbus, da Astrazeneca, sun sanar da kafa masana’antu, da kara zuba jari a kasar Sin daya bayan daya, lamarin da ya shaida cewa, kamfanonin ketare na da kwarin gwiwa game da kasar Sin, domin sun gane cewa, zuba jari ga kasar Sin shi ne kokarin kago makoma mai haske.(Kande Gao)