logo

HAUSA

Babban sakataren MDD ya yi kira ga dakarun Sudan da su tsagaita wuta yayin bikin karamar Sallah

2023-04-21 13:47:08 CMG Hausa

Babban sakataren MDD António Guterres ya yi kira ga dakarun kasar Sudan, da su tsagaita bude wuta a kalla kwanaki uku, yayin da ake murnar bikin karamar Sallah, ta yadda fararen hula za su samu tsira daga yakin da ake gwabzawa, ko jinya ga masu raunuka, ko kuma samun kayayyakin abinci da sauran muhimman ababen bukata.

Guterres ya yi kiran ne a jiya Alhamis, yayin da yake jawabi ga kafofin yada labarai, bayan kammala taro ta kafar bidiyo kan yanayin da kasar ta Sudan ke ciki, taron da kungiyar AU ta shirya a jiyan.

Babban jami’in na MDD ya ce ana iyakacin kokarin kaiwa ga tsagaita wuta. Kuma bayan an tsagaita bude wuta, dole ne bangarori daban daban na Sudan su tattuna a hukumance, su kuma kafa sabuwar gwamnatin kasa ta hanyar siyasa.

Guterres ya mai da hankali sosai kan batun asarar rayuka, da jikkatar furaren hula masu yawa, da yanayin jin kai mai tsanani, da yiwuwar habakar yakin na Sudan. Ya kuma damu da tsaron ma’aikatan MDD dake kasar ta Sudan. Don haka ya nemi bangarori daban daban na kasar da su hada kai, su matsa wa mayakan Sudan lamba, domin kaiwa ga tsagaita bude wuta.

Da yammacin jiya Alhamis, hukumar kiwon lafiya ta duniya WHO, ta fitar da sanarwa dake cewa, dauki-ba-dadi tsakanin dakarun Sudan ya riga ya haddasa mutuwar mutane a kalla 330, da kuma raunata mutane kusan 3200, wadanda suka hada da fararen hula da masu dauke da makamai. (Safiyah Ma)