logo

HAUSA

Sin ta yi kira da a goyi bayan matakan siyasa a Libya

2023-04-19 13:49:46 CMG Hausa

Mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin dake MDD Dai Bing, ya yi tsokaci yayin budadden taron kwamitin sulhun majalisar da aka shirya kan batun kasar Libya, inda ya yi kira ga sassan da abin ya shafa da su hada kai, domin ingiza gudanarwar matakan siyasa a kasar.

Dai Bing ya bayyana hakan ne a jiya Talata, yana mai cewa, a halin da ake ciki yanzu, an riga an cimma matsaya daya kan batun, cewa ya dace a daidaita halin kaka-ni-ka-yi na siyasar kasar Libya, shi ya sa ake da bukatar a hada kai don cimma nasara.

Ban da haka kuma, kamata ya yi bangarori daban daban na Libya su ci gaba da gudanar da shawarwari, domin kawar da sabanin dake tsakaninsu, ta yadda za su cimma sharadin shirya babban zabe a kasar a kan lokaci. Haka zalika, ya dace sauran kasashen duniya su samar da tallafi mai yakini, bisa ka’idar martaba burin al’ummar kasar ta Libya, tare kuma da kaucewa matsawa kasar lamba daga ketare.

Jami’in ya kara da cewa, ya kamata sassan kasa da kasa su himmantu kan aikin sake gina Libya, ta hanyar samar da karin tallafi gare ta a fannin farfado da raya tattalin aziki. Kana ya dace kwamitin sulhun MDD, da kwamitin sanya takunkumi kan Libya, su mai da hankali tare da daukar matakan da suka dace, domin daidaita matsalar hasarar kadarorin da gwamnatin kasar Libyan ke fuskanta, sakamakon matakin daskarar da kadarorin kasar da aka dauka. (Jamila)