logo

HAUSA

Sin a shirye take ta mara baya ga komawa tattaunawar zaman lafiya tsakanin Isra’ila da Falasdinu

2023-04-18 10:30:53 CMG Hausa

Dan majalissar gudanarwar kasar Sin, kuma ministan wajen kasar Qin Gang, ya ce kasarsa a shirye take ta tallafawa tattaunawar wanzar da zaman lafiya tsakanin Isra’ila da Falasdinu.

Qin Gang, wanda ya bayyana hakan a jiya Litinin, ya ce Sin na karfafa gwiwar sassan biyu da su nuna karsashin siyasa, ta yadda za su kai ga komawa teburin shawara, kuma za ta samar da zarafin cimma nasarar hakan.

A dai jiyan, Qin Gang ya zanta ta wayar tarho da takwarorinsa na Falasdinu Riad Maliki, da na Isra’ila Eli Cohen. Yayin tattaunawar tasu, Qin ya bayyana damuwar Sin game da halin zaman dar-dar da ake ciki tsakanin sassan 2. Yana mai cewa, babban burin da ake da shi a halin yanzu, shi ne dakatar da zaman doya da man ja, tare da kandagarkin ta’azzarar rikici, ko bazuwarsa ta yadda ba za a iya shawo kansa ba.

Ya ce Sin na matukar Allah wadai da duk wasu kalamai, ko daukar matakan keta hurumin kudurorin MDD, tana kuma goyon bayan komawa tattaunawar zaman lafiya tsakanin sassan biyu ba tare da bata lokaci ba, karkashin jigon kafuwar kasashe biyu masu cin gashin kansu. Har ila yau, Sin din za ta taka rawar gani wajen cimma nasarar hakan. A cewarsa, har yanzu akwai sauran lokaci na daukar matakan da suka dace.(Saminu Alhassan)