logo

HAUSA

Antonio Guterres ya yi kira da a warware tashin hankalin dake wakana a Sudan ta hanyar tattaunawa

2023-04-18 10:31:51 CMG Hausa

Babban magatakardar MDD Antonio Guterres ya yi kira ga jagororin rundunar sojin kasar Sudan da shugabannin dakarun RSF, da su gaggauta dakatar da bude wuta, su koma tekurin shawara domin warware takaddamar dake tsakaninsu ta hanyar siyasa.

Guterres ya yi wannan kira ne gabanin jawabinsa na bude taron MDD da aka shirya, domin nazartar batutuwan dake da alaka da samar da kudade domin wanzar da ci gaba.

Babban jami’in na MDD ya yi kakkausan kusa game da barkewar tashin hankali a Sudan. Yana mai cewa, tuni hakan ya haifar da mummunar asarar rayuka ciki har da na fararen hula masu yawa.

Guterres ya kara da cewa, ya zanta da jagororin sassan 2 dake dauki ba dadi, kuma yana tattaunawa da kungiyar AU, da ta kasashen Laraba ta AL da sauran jagororin shiyyar, domin shawo kan yanayin da ake ciki.  (Saminu Alhassan)