logo

HAUSA

Jami’in IMF: Bunkasuwar Sin tana ba da gudummawa ga kasar da ma daidaiton harkokin kudi a duniya

2023-04-17 12:30:00 CMG Hausa

Mataimakin daraktan sashen hada-hadar hannayen jari na asusun ba da lamuni na duniya (IMF), Fabio Natalucci ya bayyana cewa, bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin yana da muhimmanci ga zaman lafiyar kasar da ma duniya baki daya, a daidai lokacin da tsarin hada-hadar kudi na duniya ke cikin wani yanayi na damuwa.

Jami’in asusun ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua a ranar Laraba, makon jiya cewa, yana ganin ci gaba wani muhimmin tsari ne na daidaita harkokin kudi.

Natalucci wanda kuma yake kula da rahoton harkokin kudi na duniya (GFSR) ya bayyana cewa, saboda haka ci gaban kasar Sin yana da muhimmanci ga daidaiton harkokin kudi na kasar. Yana mai cewa, a matsayin wani bangare na tattalin arzikin duniya, yana da muhimmanci a farfado da bunkasuwar tattalin arzikin duniya baki daya, tare da ba da gudummawa wajen daidaita harkokin kudi.

A don haka ya ce, kasar Sin muhimmiyar kasa ce dake taka rawa a duniya, saboda gudummawar da take bayarwa ga ci gaban duniya, da yadda ake damawa da ita a kasuwar hada-hadar kudi ta duniya. Don haka a fili ya zama wajibi, kasar Sin ta taka muhimmiyar rawa wajen kokarin tinkarar wadannan matsalolin da suka shafi daidaita harkokin kudi. (Ibrahim)