logo

HAUSA

Batun leken asiri ya shaida manufar kama karya ta kasar Amurka

2023-04-16 16:33:11 CMG Hausa

A kwanakin baya ne, wasu takardun sirri da dama da ake zargin daga gwamnatin kasar Amurka suka bulla a shafukan sada zumunta. Wadannan takardu sun nuna cewa, ba wai kawai gwamnatin Amurka tana da hannu a cikin rikicin Rasha da Ukraine ba, har ma tana ci gaba da sanya ido a wasu kasashe ciki har da nata kawayenta. Wannan lamari ya janyo cece-kuce a kasashen duniya

Wani binciken ra’ayoyin jama’a da kafar CGTN ta kasar Sin ta fitar kan masu amfani da yanar gizo a duniya, ya nuna cewa, kashi 94.6 cikin dari na wadanda aka tattauna da su sun yi Allah wadai da yadda gwamnatin kasar Amurka ke nuna fuska biyu kan batun kiyaye tsaron kasa, suna ganin cewa, aikin ya shaida manufar kama karya ta kasar Amurka. Bisa binciken, kashi 91.3 cikin dari sun yi tsammanin cewa, aikin sa ido na gwamnatin kasar Amurka bai dace ba. Kashi 92.1 cikin dari sun yi tsammanin cewa, aikin ya shaida cewa kasar Amurka ta keta ikon mallakar sauran kasashe da tsaronsu. (Zainab)