logo

HAUSA

Ya kamata Amurka ta koyi hakikanin darussa daga gazawarta a Afghanistan

2023-04-14 10:07:00 CMG HAUSA

 

Mamban majalisar gudanarwar kasar Sin, kuma ministan harkokin wajen kasar Qin Gang, ya bukaci kasar Amurka ta koyi darasi daga gazawarta iri daban-daban a kasar Afganistan, kana ta canza salo ba tare da bata lokaci ba.

Qin ya bayyana hakan ne, a lokacin da yake yiwa manema labarai karin haske, bayan wata kwarya-kwaryar ganawa karo na biyu da aka yi, tsakanin ministocin harkokin wajen kasashen Sin, da Rasha, da Pakistan da kuma Iran. An kuma bukace shi da ya yi karin bayani kan wani rahoton bincike da fadar White House ta fitar a farkon wannan wata, kan janyewar Amurka daga Afghanistan, wadda ta amince da "gagarumin gazawar leken asiri" da kuma dora alhakin janyewar kan gwamnatin da ta gabata.

Qin ya jaddada cewa, janyewar soji ba ya nufin yin watsi da alhakin da aka dora mata, haka kuma rahoton ba ya nufin kawo karshen munanan ayyukan da Amurka ta aikata a kasar Afganistan. Ya kara da cewa, bai kamata Amurka ta yi kasa a gwiwa, ta kuma rufe ido kan wahalhalun da al'ummar Afganistan ke ciki ba, kuma wajibi ne a hanzarta mayar da kudaden da aka kwace da karfin tuwo daga Afghanistan.

Qin ya ce, yana fatan Amurka za ta iya koyon darussa bil hakki da gaskiya daga abin da ya faru a tarihi, da kuma canja salo nan da nan, maimakon yin amfani da ka'idojin kasashen yamma wajen yanke hukunci da tsoma baki a cikin tsarin wasu kasashe, ko yunkurin sake tura dakarun soji cikin Afghanistan da kuma yankin, balle ma tallafawa da ma yin amfani da ta'addanci don neman cimma wata manufa ta kashin kai. (Ibrahim Yaya)