logo

HAUSA

Sanarwar hadin gwiwa ta kwarya-kwaryar taro na 2 game da Afghanistan tsakanin ministocin wajen Sin da Rasha da Pakistan da Iran

2023-04-14 22:17:01 CMG Hausa

A jiya Alhamis ne ministocin wajen Sin, da Rasha, da Iran, da Pakistan, suka gudanar da taro na 2 game da Afghanistan, a birnin Samarkand na kasar Uzbekistan.

Yayin taron, ministocin sun jaddada muhimmancin martaba ikon mulkin kai, da ‘yanci da kimar yankunan Afghanistan, da goyon bayan al’ummar Afghanistan su mulki kasar su, wanda hakan zai baiwa kasar damar cimma burikan ta na siyasa a nan gaba, da zabar hanyar ci gaba da kasar ta zama.

Kaza lika, sun bukaci sassan kasa da kasa da su kare moriyar zaman lafiya da daidaito a Afghanistan, kasar da suka bayyana a matsayin wadda ya dace a yi hadin gwiwa domin ingiza ci gaban ta, maimakon mayar da ita dandalin adawar siyasar shiyya.

Har ila yau, ministocin sun jaddada cewa, ta hanyar tattaunawa da shawarwari ne kadai za a iya kaiwa ga warware batun siyasar Afghanistan. Sun kuma jaddada adawar su ga sake kafa sansanonin sojoji a Afghanistan da kewayen ta, musamman daga kasashen da su ne suka jefa kasar cikin halin da take a yanzu, yanayin da ko kadan, ba zai haifar da da mai ido ga zaman lafiya da daidaito a shiyyar ba. (Saminu Alhassan)