logo

HAUSA

Sin na son yin aiki tare da kasar Rasha don kiyaye dangantakar dake tsakanin kasashen biyu

2023-04-14 10:09:55 CMG HAUSA

 

Mamban majalisar gudanarwar kasar Sin kuma ministan harkokin wajen kasar Qin Gang, ya bayyana yayin ganawarsa da takwaransa na kasar Rasha Sergei Lavrov jiya Alhamis a birnin Samarkand na kasar Uzbekistan cewa, a shirye kasarsa take ta yi aiki tare da Rasha, domin kiyaye dangantakar dake tsakanin kasashen biyu.

Qin ya bayyana cewa, ba da dadewa ba ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya kai ziyarar aiki a kasar Rasha cikin nasara, tare da samun sakamako mai kyau, wanda ya ba da jagoranci bisa manyan tsare-tsare da martaba muhimman tsare-tsare na zurfafa hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Rasha a sabon zamani.

Ya kara da cewa, kasar Sin na son yin aiki tare da kasar Rasha, domin daukar wani muhimmin aiki na aiwatar da yarjejeniyar da shugabannin kasashen biyu suka cimma.

Ya ce, ya kamata bangarorin biyu su ci gaba da zurfafa mu'amala, da kiyaye amincewar juna a fannin siyasa, da sa kaimi ga shirin raya fifiko a fannin hadin gwiwa tsakanin Sin da Rasha nan da shekarar 2030, da shugabannin kasashen biyu suka sanyawa hannu don ganin ta fara aiki ba tare da bata lokaci ba, da kuma ba da jagoranci wajen samun bunkasuwa mai inganci na hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya tsakanin kasashen biyu.

A nasa bangare kuwa, Lavrov ya bayyana cewa, yawan cudanya da daidaita manyan tsare-tsare tsakanin Rasha da Sin, na nuna kyakkyawan ci gaba da tsayin daka kan dangantakar dake tsakanin kasashen biyu. (Ibrahim Yaya)