logo

HAUSA

Wakilin Sin ya yi kira da a kara goyon bayan kokarin da ake yi na yaki da ta'addanci da samar da kwanciyar hankali a Mali

2023-04-13 10:58:00 CMG Hausa

Zaunannen wakilin kasar Sin a MDD Zhang Jun ya yi kira ga kasashen duniya da su goyi bayan kokarin da ake yi na yaki da ta'addanci a kasar Mali.

Zhang Jun wanda ya bayyana hakan yayin taron kwamitin sulhu na MDD game da tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD a kasar Mali (MINUSMA), ya kuma jaddada muhimmancin goyon bayan kasa da kasa ga kokarin kasar Mali, na yaki da ta'addanci da tabbatar da zaman lafiya. Yana mai cewa, wannan shi ne abu mafi muhimmanci.

Jakadan ya ce, wajibi ne MINUSMA ta sauke nauyin da kwamitin sulhu na MDD ya damka mata, ta kuma goyi bayan dukkan sassa.

Zhang ya ce, tilas ne tawagar MINUSMA ta ba da karin tallafi a fannonin da suka hada da ganin dukkan sassa sun martaba ka'idojin tsagaita bude wuta, da ciyar da shirin kwance damara, da sake hadewa, da kara karfin jami'an tsaron kasar gaba.

A yayin da yake karin haske kan tsarin siyasa a kasar, Zhang ya ce, mahukuntan Mali sun shiga tattaunawa mai zurfi da bangaori, kuma sun yi ayyuka da dama wajen tsara kundin tsarin mulkin kasar, da shirye-shiryen gudanar da babban zabe, da makamantansu.

Jakadan ya bayyana cewa, kasar Sin tana goyon bayan kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka a ci gaba da kokarin shiga tsakani bisa tushen mutunta 'yancin kai da cikakkun yankunan kasar Mali. (Ibrahim Yaya)