logo

HAUSA

MDD ta sanar da shirin baiwa kasar Chadi agajin jin kai na dalar Amurka miliyan 674

2023-04-13 11:02:07 CMG Hausa

MDD ta kaddamar da wani shirin bayar da agajin dalar Amurka miliyan 674 jiya Laraba don taimakawa mutane miliyan 4.4 a kasar Chadi, daya daga cikin kasashe mafi fama da talauci a duniya.

Ofishin kula da harkokin jin kai na MDD ko OCHA a takaice, ya ce daga bara kadai, adadin masu bukata a kasar Chadi ya haura da kusan dubu 800, cikin jimillar mutane miliyan 6.9 da suka hada da ’yan gudun hijira da wadanda suka dawo cikin kasar da wadanda suka bar muhallansu.

A cewar ofishin, karuwar ta faru ne sakamakon mummunar ambaliyar ruwa a shekarar da ta gabata, da rashin tsaro, da matsalar sauyin yanayi, da tabarbarewar tattalin arziki sanadiyar annobar COVID-19, da kuma yakin Ukraine da ya shafi farashin abinci.

OCHA ya jaddada cewa, tilas ne a samar da isassun kudade kan rokon da aka gabatar a bana, inda ya kara da cewa, kaso 60 cikin 100 kadai shirin ya samu, cikin kudaden da yake bukata wajen aiwatar da agajin jin kai na shekarar 2020, inda masu aikin jin kai suka samu damar kaiwa ga mutane miliyan 2.2.  (Ibrahim Yaya)