logo

HAUSA

IMF: Tattalin arzikin Sin zai karu da kaso 5.2 a 2023

2023-04-12 10:05:21 CMG Hausa

Asusun bada lamuni na duniya IMF ya yi hasashen cewa, tattalin arzikin kasar Sin a bana, zai karu da kaso 5.2 cikin dari, sannan kuma zai karu da kaso 4.5 cikin dari a shekarar 2024.

Daraktan sashen bincike na asusun, Pierre-Oliver Gourinchas ne ya bayyana haka, yayin wani taron manema labarai a jiya Talata, inda ya gabatar da sabon rahoton hasashen tattalin arzikin duniya da asusun na IMF ya yi.

A cewarsa, karfin tattalin arzikin kasar Sin, zai kasance muhimmiyar gudummawa ga ci gaban tattalin arzikin duniya a shekara mai zuwa. Yana mai cewa, wani muhimmin batu a bana shi ne, tattalin arzikin Sin na kara habaka cikin sauri kuma cike da kuzari. (Fa’iza Mustapha)