logo

HAUSA

Jim Rogers: Ana duba yuwuwar kara zuba jari a kasar Sin

2023-04-12 11:22:18 CMG Hausa

Sanannen masanin harkokin kudi da zuba jari na duniya Jim Rogers, ya ce ana duba yuwuwar kara zuba jari a kasar Sin yayin da ake hasashen makoma a nan gaba.

Jim Roger ya ce, yana da hannun jari a kasar Sin, kuma yana kokarin kara zuba jari a kasuwar hannayen jari ta kasar.

Masanin wanda ya shafe shekaru sama da 20 yana zuba jari a kasar Sin, ya bayyana haka ne cikin jawabin da ya gabatar a yayin taron tattaunawa na bana, na jami’ar Yale ta Amurka da kasar Sin a makon da ya gabata, inda ya jaddada muhimmancin kasar Sin a karni na 21.

A cewarsa, idan masu zuba jari za su yi bincike, to akwai dimbin damarmaki a kasar Sin, bisa la’akari da yawan al’ummarta, kuma rashin bashi mai girma da ake binta da gibin cinikayya, sun tallafa sosai ga takardar kudin kasar wato RMB. (Fa’iza Mustapha)