logo

HAUSA

Manyan kasashe masu tasowa na duniya biyu sun kara yin mu’amala da juna

2023-04-12 10:20:12 CMG Hausa

Sin da Brazil, manyan kasashe masu tasowa biyu mafiya girma ne a rabin gabashin duniya da rabin yammacin duniya. Yayin da shugaban kasar Brazil Luiz Inacio Lula da Silva ya fara ziyara a kasar Sin a yau, wadannan kasashe biyu sun kara yin mu’amala da juna.

Bisa kokarin manyan shugabannin kasashen biyu, an zurfafa hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Brazil, kana jama’ar kasashen biyu sun kara sada zumunta da juna. Abu na musamman shi ne, hadin gwiwar kimiyya da fasaha ya kasance muhimmi yayin da ake raya hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu. Game da wannan fanni, aikin tauraron dan Adam na binciken albarkatun duniya na Sin da Brazil ya kasance abin misali na hadin gwiwar dake tsakanin kasashe masu tasowa, wanda ya karya kane-kane a fannin fasahohi da kasashe masu ci gaba suka yi.

Kasashen biyu sun kiyaye hadin gwiwa a cikin kungiyoyin kasa da kasa da tsarin bangarori daban daban kamar su MDD, da hukumar cinikayya ta duniya wato WTO, da kungiyar G20, da kungiyar BRICS da sauransu, kuma sun daga muryar kasashe masu tasowa da burin samun ci gaba cikin lumana a duniya.

Kasa da kasa sun maida hankali sosai ga ziyarar shugaban kasar Brazil Lula a kasar Sin a wannan karo. A matsayin manyan kasashe masu tasowa a duniya, bunkasuwar dangantakar dake tsakanin Sin da Brazil ta kawo moriya gare su, har ma ga duk duniya baki daya. An yi imanin cewa, bisa jagorancin shugabannin kasashen biyu, za a inganta hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Brazil a fannoni daban-daban, kuma hakan zai samar da sabuwar gudummawa wajen samun zaman lafiya da wadata a yankinsu da duniya baki daya. (Zainab)