logo

HAUSA

Amurka na ci gaba da sanya ido kan abokanta

2023-04-11 11:21:19 CMG Hausa

Rahotanni daga kafafen yada labaran Amurka na cewa, a baya-bayan nan, wasu takardun sirrin sojojin Amurka sun bayyana a shafukan sada zumunta da dama. Wadannan takardu sun nuna cewa, gwamnatin Amurka ba wai kawai tana da hannu a rikicin kasashen Rasha da Ukraine ba, har ma tana ci gaba da sanya ido sosai kan kawayenta, da suka shafi Isra'ila, da Koriya ta Kudu da sauran kasashe.

Dangane da rahotannin da Amurka ta sanyawa idanu, yayin da suke mayar da martani kan wannan batu jiya, 'yan majalisar jam'iyyar adawa ta Koriya ta Kudu sun bayyana "damuwa matuka", suna ganin cewa, ko shakka babu hakan cin zarafi ne ga Koriya ta Kudu da kuma "gazawar” gwamnatin Koriya ta Kudun mai ci wajen tabbatar da tsaron kasa. Suna masu kira da a gudanar da cikakken bincike kan wannan lamari.

Shekaru da dama, an sha kiran Amurka a matsayin "Babbar daula mai sanya ido a duniya”, inda ta rika sanya ido kan kasashen duniya, kan masu fafutuka da ma kawayenta, har ma da shugaban gwamnatin Jamus, da shugaban Faransa da sauran shugabanni kawayenta. (Ibrahim Yaya)