logo

HAUSA

Shugaban Bankin Duniya: Sin da Indiya sun tsallake koma bayan da tattalin arzikin duniya zai fuskanta a bana

2023-04-11 14:01:09 CMG Hausa

Shugaban bankin duniya David Malpass ya bayyana cewa, kasashen Sin da Indiya sun fita da rukunin koma bayan da ake hasashen tattalin arzikin duniya zai fuskanta a bana.

Malpass ya bayyana hakan ne gabanin taron asusun ba da lamuni na duniya (IMF) da Bankin Duniya, kamar yadda wata sanarwar manema labarai da aka wallafa a shafin yanar gizon bankin mai suna worldbank.org jiya Litinin.

MalPass ya ce, ana sa ran ci gaban duniya zai yi rauni a bana, inda zai ragu zuwa kashi 2 cikin 100 daga kashi 3.1 cikin 100 a shekarar 2022. Yana mai cewa, ci gaban GDPn Sin zai karu zuwa kashi 5 bisa dari a shekarar 2023, baya ga karuwar zuba jari.

Ya kara da cewa, ya lura da daidaiton harkoki da manufofinta na hada-hadar kudi yadda ya kamata. (Ibrahim Yaya)