logo

HAUSA

Sin na adawa da tsoma baki a harkokin cikin gidan wasu kasashe ta hanyar fitar da makamai

2023-04-11 11:15:12 CMG HAUSA

 

Jiya ne bisa agogon wuri, aka kira wani taro mai taken “Hadarin da matakin sabawa yarjejeniyar fitar da makamai da na’urorin soja zai haifar” bisa bukatar Rasha, kasar dake rike da shugabancin karba-karba na kwamitin sulhu na MDD. Yayin taron, wakilin na kasar Sin ya jaddada cewa, ya zama wajibi a daina tsoma baki a harkokin cikin gidan wasu kasashe, ta hanyar amfani da makaman da ake fitarwa zuwa kasashen waje, da kuma mara baya ga masu neman kawo baraka.

Mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin a MDD Geng Shuang, ya bayyana cewa, tilas ne mu yi kakkausar suka tare da yin adawa da amfani da makaman da ake fitarwa zuwa kasashen waje, domin cimma muradun kashin kai na siyasa. Ya kara da cewa, kasar dake da karfi a fannin soja, ta dade tana fitar da dimbin kayayyakin soja zuwa wasu kasashe bisa tsarin takaita fitar da makaman ga sauran kasashe marasa karfi. Sin na yin kira ga kasashen duniya, musamman ma kasashen dake karfin soja, da su sauke nauyin dake wuyansu, da aiwatar da manufar fitar da makamai zuwa ketare yadda ya kamata, da daina amfani da kayayyakin da ake fitarwa zuwa kasashen waje, wajen tsoma baki a harkokin cikin gidan wasu kasashe. (Amina Xu)