logo

HAUSA

Jami’an Saudiyya sun isa Iran don tattaunawa kan sake bude ofisoshin jakadanci

2023-04-09 16:36:16 CMG Hausa

Rahotanni daga ma’aikatar harkokin wajen kasar Saudiyya sun ce, wasu jami’an ta sun isa birnin Tehran na kasar Iran jiya Asabar, inda suka gudanar da shawarwari tare da jami’an kula da harkokin karbar baki na ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran, kan batutuwan da suka shafi sake bude ofisoshin jakadancin Saudiyya. Saudiyya ta godewa Iran saboda yadda ta karbi jami’anta, su kuma jami’an Iran sun jaddada niyyar su ta samar da duk wani sauki ga jami’an Saudiyya don su gudanar da ayyukan su yadda ya kamata a Iran.

Rahotanni daga kafafen yada labaran kasar Iran sun ce, makasudin ziyarar jami’an Saudiyya a wannan karo shi ne, tattaunawa kan sake bude babban ofishin jakadancin Saudiyya dake birnin Tehran, gami da karamin ofishin jakadancin ta a Mashhad, birni na biyu mafi girma a Iran. (Murtala Zhang)