logo

HAUSA

Bai kamata Birtaniya ta yi biris da batun ikon mallakar tsibiran Malvinas ba

2023-04-04 10:59:13 CMG Hausa

A ranar Lahadi 2 ga watan Afrilun nan ne aka gudanar da bikin tunawa da yakin tsibiran Malvinas, yakin da ya faru shekaru 41 da suka gabata.

A yayin bikin, shugaban kasar Argentina Alberto Fernández, ya wallafa wani gajeren bidiyo, tare da fitar da wani rubutu dake cewa, tsibiran Malvinas yanki ne na kasar sa. Ya ce Argentina ta sake bayyana bukatarta ta warware batun tsibiran Malvinas ta hanyar tattaunawa, bisa wasu kudurorin MDD masu nasaba da hakan. Game da wannan, bai dace ‘yan siyasar Birtaniya su ci gaba da yin biris da bukatun ba.

A zahiri, batun tsibiran Malvinas batu ne a sanadin mulkin mallaka. A shekarar 2016, “Kwamitin kula da yankunan nahiyoyi da ke daura da teku” na MDD ya yanke shawarar cewa, tsibiran Malvinas suna cikin yankunan tekun da Argentina ta mallaka. Kaza lika, taron da kwamitin musamman mai adawa da mulkin mallaka na MDD ya gudanar, ya taba yi wa gwamnatin Birtaniya matsin lamba, da ta gudanar da tattaunawa tare da Argentina, amma bangaren Birtaniya ya ki amincewa da yin hakan.

Ya kamata a san cewa, ba za a koma zamanin mulkin mallaka ba. Kuma bai dace tsofaffin ‘yan mulkin mallaka su kawar da ido daga batun Argentina kuma su ci gaba da cin moriya daga mulkin mallaka da suka kafa ba. Dole ne bangaren Birtaniya ya amsa bukatu na jama’ar Argentina, na mayar musu tsibiran Malvinas.(Safiyah Ma)