logo

HAUSA

Sin za ta samarwa duniya sabbin damammaki ga bunkasuwarta

2023-04-04 20:21:09 CMG HAUSA

 

Dangane da rahoton da bankin duniya ya fitar, mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning ta bayyana cewa, kasar Sin za ta ci gaba da kara bude kofarta ga kasashen waje, da samar da karin tabbaci da kwanciyar hankali da karin tsaro ga duniya, kuma sabon ci gabanta, zai kara samar da sabbin damammaki ga duniya.

A kwanakin baya ne, bankin duniya ya fitar da rahoton watan Afrilu na bunkasuwar tattalin arziki a yankin gabashin Asiya da tekun Pacific a watanni 6 na farkon shekarar 2023. Idan ya yi hasashe cewa, saurin bunkasuwar tattalin arzikin wannan yanki zai karu da kashi 5.1%, saboda yadda tattalin arzikin kasar Sin ke farfadowa matuka

Ban da wannan kuma, Mao Ning ta mai da martani game da kiran da shugabar kwamitin EU Ursula von der Leyen ta yi kan kasar Sin na daukar matakin da ya dace wajen magance rikicin Ukraine, ta ce, Sin na fatan kara mu’ammala da EU don warware rikicin a siyasance.

Haka kuma, Mao Ning ta nanata cewa, Sin na adawa da ziyarar Cai Yingwen a Amurka da ba bisa gaskiya da dokar kasar Sin ba. Sin na matukar adawa da ganawar shugaban majalisar wakilan Amurka Kevin McCarthy da Cai. (Amina Xu)