logo

HAUSA

Mambobin OPEC+ sun sanar da kudirin su na kara rage yawan danyen mai da suke hakowa

2023-04-03 14:31:45 CMG Hausa

Masarautar Saudiyya da sauran kasashe masu fitar da danyen mai zuwa kasuwannin duniya ko OPEC+, sun sanar da kudurinsu na kara rage danyen mai da suke fitarwa, da kusan ganga miliyan 1.16 a ko wace rana, matakin da masharhanta ke cewa zai iya daga farashin danyen man a kasuwannin duniya, duk da cewa Amurka a nata bangare ta nuna rashin gamsuwa da hakan.

Kamfanin dillancin labarai na Reuters, ya lasafta jimillar adadin danyen man da kasashen suka amince su rage zuwa ganga miliyan 3.66 a duk rana, adadin da zai kai kaso 3.7 bisa dari na bukatar man a duniya baki daya.

Kasar Saudiyya dake sahun gaba a fannin fitar da danyen man, ta ce za ta rage ganga 500,000 a ko wace rana. Matakin da ma’aikatar man kasar ta ce na kandagarki ne, zai kuma tallafa wajen daidaita farashin mai a kasuwannin duniya. Sauran kasashen da suka amince su rage yawan man da suke hakowa bisa rashin kan su, sun hada da hadaddiyar daular larabawa, da Kuwait, da Iraqi, da Oman da Aljeriya.

Sanarwar ta jiya Lahadi ta zo ne kwana guda, kafin taron yanar gizo na ministocin kungiyar ta OPEC+, wanda a baya aka yi tsammanin zai tabbatar matsayar kungiyar na da rage hako ganga miliyan 2 duk rana, wanda dukkanin kasashe mambobin kungiyar suka aminta da shi har zuwa karshen wannan shekara ta 2023.  (Saminu Alhassan)