Ronaldo ya kafa tarihin yawan buga wasa a tawaga a duniya
2023-04-02 16:16:35 CRI
Kane ya zama kan gaba a yawan ci wa Ingila kwallaye a tarihi
Wanda aka sabunta Sa'o'i 5 da suka wuce
Harry Kane ya zama kan gaba a yawan ci wa Ingila kwallaye mai 54, bayan da Ingila ta ci Italiya 2-1 a wasan shiga Euro 2024.
Kane, mai shekara 29 ya yi kan-kan-kan da Wayne Rooney mai rike da tarihin a gasar kofin duniya a Qatar, bayan da ya ci Faransa a wasan da aka fitar da su a quarter finals.
Ya kuma cin kwallon ranar Alhamis a bugun fenariti a karawar hamayya da suka yi a Naples, filin wasa na Diego Maradona.
Kenan Kane ya zama kan gaba a yawan cin kwallaye a tawagar Ingila da kuma Tottenham.
Ya kuma ci wa Ingila kwallo 54 a karawa 81 da ya yi wa tawagar.
Declan Rice ne ya fara ci wa Ingila kwallo a minti na 13 da fara wasa, yayin da Italiya ta farke ta hannun Mateo Retegui, bayan da suka koma zagaye na biyu.
Ingila ta karasa wasan da 'yan kwallo 10 a cikin fili, bayan da aka bai wa Luke Shaw jan kati, saura minti 10 a tashi daga wasan na hamayya.
Ga jerin 'yan wasan Ingila da suka ci mata kwallo sama da 40:
Harry Kane (Daga 2015) Ya ci kwallo 54 a wasa 81
Wayne Rooney (2003-2018) Ya ci kwallo 53 a wasa 120
Bobby Charlton (1958-1970) Ya ci kwallo 49 a wasa 106
Gary Lineker (1984-1992) Ya ci kwallo 48 a wasa 80
Jimmy Greaves (1959-1967) Ya ci kwallo 44 a wasa 57
Michael Owen (1998-2008) Ya ci kwallo 40 a wasa 89
Cikin kwallayen da Kane ya ci har da shida da ya zura a raga a gasar kofin duniya a Rasha, wanda ya zama na uku dan kasar da ya lashe takalmin zinare a babbar gasar tamaula a duniya.
Na farko mai bajintar shine Garry Lineker a gasar kofin duniya a 1986 da kuma Alan Shearer a gasar nahiyar Turai a 1996
Ya kuma kafa tarihi da yawa a tawagar Ingila, wanda ya ci 16 a farkon shekarar 2021 zuwa karshenta.
Kane yana da jan aiki a gabansa idan yana fatan kalubalantar Cristiano Ronaldo mai kwallo 120 a yawan zura wa tawaga a tarihi.
Kwallo 204 da ya zura a raga a Tottenham ya zama na uku a jerin wadanda ke kan gaba a cin kwallaye a Premier League.
Ronaldo ya kafa tarihin yawan buga wasa a tawaga a duniya
Cristiano Ronaldo ya buga wa Portugal wasa na 197, ya kuma ci kwallo biyu a wasan neman shiga Euro 2024, bayan doke Liechtensen 4-0.
Mai shekara 38, shine kan gaba a yawan cin kwallaye a tawaga a tarihi mai 120 kawo yanzu.
Ya fara yi wa Portugal tamaula a 2003, wanda a gasar kofin duniya a Qatar a 2022 ya zama na farko da ya zura kwallo a kowacce gasa biyar a kofin duniyar.
Minti takwas da fara wasa Portugal ta ci kwallo ta hannun Joao Cancelo, minti biyu da komawa zagaye na biyu Bernardo Silva ya kara na biyu.
TALLA
Sai Cristiano Ronaldo ya ci na uku a bugun fenariti, sannan ya kara na hudu na biyu da ya zura a raga a wasan.
A gasar kofin duniya a Qatar da Ronaldo ya buga, shine ya yi kan-kan-kan da Bader Al-Mutawa, wanda ya yi wa Kuwai fafatawa 196.
Ronaldo ya yi kafada da dan kwallon Kuwat a yawan buga wa tawaga tamaula a wasan da Morocco ta fitar da Portugal a zagayen quarter finals.
Mai Ballon d'Or biyar ya yi zaman benci a Qatar a Porugal, sai dai sabon koci, Roberto Martinez ya gayyaci tsohon dan wasan Real Madrid da Juventus.
Ronaldo ya koma taka leda a gasar kwallon kafa ta Saudi Arabia a Al Nassr a watan Janairu, bayan da ya raga gari da Manchester United.
Uefa za ta binciki Barcelona kan sayen wasanni
Uefa za ta yi bincike kan Barcelona, sakamakon kudin da ta biya tsohon mataimakin shugaban kwamitin rafli a Sifaniya.
Tuni hukumar ta nada jami'in da zai yi bincike kan kudin da ake zargin Barcelona ta yi don ta samu sakamakon wasannin da zai amfane ta.
An shigar da karar Barcelona kan tuhumar cin hanci da bayar da rahoton karya da aikata rashin gaskiya.
Masu shigar da kara na tuhumar Barcelona da biyan fam miliyan 7.1 ga Jose Maria Enrique Negreira da kamfaninsa Dasnil 95.
Barcelona wadda ta musanta aikata ba daidai ba ta ce ta biya kudin ga Dasnil 95 tsakanin 2001 zuwa 2018.
Uefa ta ce: "Ta nada jami'in da zai binciko ko Barcelona ta karya dotar hukumar kan kudin da ake zargin ta biya Caso Negreira.''
Wani gidan rediyo ne mai suna Ser Catalunya ya bayar da rahoton biyan kudin daga nan mahutuntan karbar haraji suka fara bibiyar Dasnil 95.
"Barcelona ta cimma yarjejeniyar baka da baka a boye da Jose Maria Enriquez Negreira a matakinsa na mataimakin kwamitin alkalan tamaula a Sifaniya da biyansa kudi domin kungiyar ta amfana da samakon wasanni,'' in ji masu shigar da kara a Sifaniya.
Barcelona ta ce ta biyan kudin ne domin a hada mata rahoto a faifan bidiyo kan yadda alkalan ke gudanar da aikinsu, kamar yadda kociyoyonta suka bukata, don taimaka musu wajen gudanar da aiki.
Wadanda ake tuhuma sun hada da tsohon shugaban Barcelona, Josep Maria Bartomeu da Sandro Rosell da kuma Negreira.
Ofishin masu shigar da kara ne ya kai batun kotu, domin a tuhumi Barcelona.
Shugaban gasar La Liga, Javier Tebas ya ce ya kamata shugaban Barcelona na yanzu, Joan Laporta ya yi murabus idan ya kasa bayani kan wannan tuhumar.
Real Madrid ta ce tana goyon bayan a tuhumi Barcelona, sannan a shirye take ta bayar da sheda a gaban kotu, domin ta kare martabar ta.