logo

HAUSA

Hauhawar farashin Dala da tsadar man jirgi zai iya shafar farashin aikin hajji ga alhazan duniya a bana

2023-04-02 09:32:53 CMG Hausa

Yayin da musulmin kasashen duniya ke shirye-shiryen aikin hajjin 2023, masu ruwa da tsaki kan aikin hajji da wasu daga cikin maniyata sun fara bayyana fargabar ta`azzarar farashin aikin hajjin a bana.

Kasar Saudiya dai ta sanar cewa a bana tana sa rana karbar mahajjata sama da miliyan uku ninki biyu na adadin alhazan data saba karba a duk shekara.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.