logo

HAUSA

Ministan wajen Syria ya ziyarci Masar a karon farko cikin sama da shekaru 10

2023-04-02 15:39:38 CMG Hausa

Rahotanni daga kasar Masar na cewa, ministan harkokin wajen kasar Sameh Shoukry, jiya Asabar ya tattauna da takwaransa na kasar Syria Faisal Mekdad, wanda ke ziyara a birnin Alkahira, a karon farko cikin fiye da shekaru 10.

A cikin wata sanarwa da kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Ahmed Abu Zeid ya fitar na cewa, ministocin biyu sun tattauna batutuwa daban-daban da suka shafi alakar da ke tsakanin kasashen biyu, da matakan kara inganta su, baya ga wasu batutuwan da suka shafi shiyya-shiyya da kasa da kasa dake shafar moriyarsu ta bai daya

Minista Shoukry ya nanata cikakken goyon bayan Masar, kan kokarin da ake yi na cimma cikakken sulhu na siyasa da ma sulhuntawa a Syria.

A nasa banaren kuwa, Mekdad ya bayyana jin dadin kasarsa, kan rawar da Masar ta taka a cikin shekaru da suka gabata, da kuma taimakon agajin jin kai da Masar din ta bayar, biyo bayan mummunar girgizar kasar da ta afku a Siriya a watan Fabrairu.

Ministan harkokin wajen kasar Syria ya ce, yana fatan kara samun hadin kai tsakanin Larabawa da kasar Syria, domin shawo kan rikicin da ke damunta da kuma dawo da rawar da take takawa a tarihi wajen tallafawa kasashen Larabawa.

Kasashen Larabawa da dama ne suka juyawa kasar Syria baya, da ma dakatar da ita daga zama mambar kungiyar hada kan kasashen Larabawa, tun bayan barkewar rikicin Syria a shekara ta 2011.(Ibrahim)