logo

HAUSA

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Da Suka Mallaki Makaman Nukiliya Su Rage Barazanar Barkewar Yaki

2023-04-01 16:32:00 CMG Hausa

Mataimakin zaunannen wakilin Sin a MDD Geng Shuang, ya bayyana kiran kasarsa ga dukkan kasashen da suka mallaki makaman nukiliya, da su rage barazanar barkewar yaki.

Geng Shuang ya bayyanawa taron kwamitin tsaro kan barazanar da zaman lafiya da tsaro ke fuskanta a duniya cewa, aminci da hadin gwiwa tsakanin manyan kasashe, shi ne ginshikin tabbatar da kwanciyar hankali mai inganci a duniya.

Ya kara da cewa, a watan Janairun bara, shugabannin kasashe 5 da suka mallaki makaman nukiliya, sun fitar da sanarwar hadin gwiwa, inda suka jaddada cewa, ba za a taba nasara a yakin nukiliya ba, kuma bai kamata ma a yi shi ba. Haka kuma sun tabbatar da cewa, ba sa shirin kai wa juna hari ko ma sauran kasashe.

A cewarsa, bisa la’akari da yanayin dangantakar wadannan kasashe a yanzu, wannan muhimmiyar sanarwa, ta na da matukar muhimmanci fiye da kowanne lokaci. 

Ya ce, kasar Sin na bayar da muhimmanci ga matsayin yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukiliya a wani mataki na kwance damarar makamai da hana yaduwarsu, da kokarin yayata yadda za a dauki matakai daki-daki wajen samun nasarar rage makaman nukiliya har zuwa lokacin da za a haramta su da ma kawar da su baki daya. (Fa’iza Mustapha)