logo

HAUSA

Dan siyasar Zambia: “Taron kolin diplomasiya” ba zai canja “makircin diplomasiyar Amurka” ba

2023-03-30 10:40:29 CMG Hausa

Shugaban jam’iyyar 3rd Liberation Movement ta Zambia, Enock Tonga, ya yi tsokaci game da “taron kolin diplomasiya” da Amurka ta sake gudanarwa a kwanakin nan, inda ya ce Amurka ta saba da kiran kanta a matsayin “misalin diplomassiya”, amma ra’ayin danniya da take bi ya lalata tsarin kasa da kasa sosai, a sa’i daya kuma, ta yi biris da dukkan abubuwa marasa kyau dake faruwa a kasar, abun da ya shaida cewa “diplomasiyar Amurka” ba ta da gaskiya ko kadan.

Enock Tonga bayyana haka ne yayin da yake zantawa da wakilin CMG, inda ya kara da cewa, galibin ayyukan da Amurka ta ke yi, tana yin su ne don moriyar kanta kawai, yana mai cewa, ba ta taba yin la’akari da ci gaban sauran kasashen duniya ba. (Safiyah Ma)