logo

HAUSA

Tallafin Likitocin Sin A Rwanda Ya Samu Yabo Daga Al’ummun Kasar

2023-03-30 19:50:43 CMG Hausa

Cikin shekaru da dama, likitocin kasar Sin na baiwa al’ummun sassa daban daban na nahiyar Afirka tallafin jinyar nau’o’in cututtuka dake addabar su musamman marasa karfi, da mata, da kananan yara. Wannan mataki ne dake dada tabbatar da kyakkyawan zumunci, da ingancin dangantakar kasar Sin da aminan ta na kasashe masu tasowa.

Karkashin irin wannan tallafi, na tawagogin kiwon lafiyar kasar Sin masu ba da jinya a kasashen Afirka, a kwanan nan tawaga ta 23, ta jami’an lafiyar Sin da aka tura kasar Rwanda, ta gudanar da ayyukan jinya, da rarraba fasahohin kashe radadin ciwo tare da takwarorin su na kasar Rwanda.

A farkon makon nan ne likitocin na Sin suka kafa cibiyar su a asibitin Masaka, dake wajen birnin Kigali fadar mulkin kasar, albarkacin bikin “Makon Alluran Kashe Radadin Ciwo na Kasar Sin” wanda ake gudanarwa duk shekara a kasar Sin.

Albarkacin wannan biki, tawagar jami’an lafiyar na Sin da takwarorin su na Rwanda, sun gudanar da tattaunawar karawa juna sani, game da alluran kashe radadin ciwo ta yanar gizo, tare da wasu likitoci dake aiki a wani asibiti dake jihar Mongolia ta gida ta arewacin kasar Sin, domin yayata sanin makamar aiki, dangane da dabaru mafiya dacewa na amfani da nau’o’in alluran kashe radadin ciwo, musamman yayin ayyukan tiyata.

Yadda dubban mazauna yankin suka fito zuwa cibiyar da aka kafa domin samun jiyya kyauta, ciki har da duba yanayin bugun jini, da awon sikari, da yawan kitse a jiki, tare da zantawa da masana kiwon lafiya game da lafiyar su, ya nuna gamsuwar da al’ummun kasashen da suke samun irin wannan tallafi ke nunawa, ga ayyukan tawagogin jami’an lafiyar kasar Sin.

Ko shakka babu, hakan na kara gaskata imanin da al’ummun Afirka ke da shi dangane da tallafin kiwon lafiya daga likitocin Sin, kana hakan na kara jaddada alkawuran da Sin ta jima tana yi ga ‘yan uwan ta na kasashe masu tasowa, cewa burin ta shi ne samar da al’ummar duniya mai kyakkyawar makomar bai daya, manufar da har kullum ke shan yabo daga al’ummun kasa da kasa, musamman ma na kasashe masu tasowa.(Saminu Alhassan)